in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta bullo da sabon tsari game da tallafin mai a kasar
2016-05-11 10:36:52 cri

Gwamnatin Najeriya za ta bullo da sabon salo game da batun tallafin mai a kasar nan da kwanaki kadan masu zuwa, da nufin kawo sauyi a harkar tallafin man.

Ministan albarkatun mai na kasar Ibe Kachickwu, shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin halartar taron tattaunawa da al'umma da aka gudanar a arewacin jihar Kaduna, ya kara da cewa, yin kwaskwarima game da farashin mai zai kawo karshen matsalar man da ta jima tana addabar kasar.

Minsitan ya fada cewar, wajibi ne sashen dake kula da albarkatun man kasar ya gudanar da tsari da ya dace da tsarin farashin mai a kasuwannin duniya.

Game da batun aikin hako man fetur a yankin arewacin kasar kuwa, minsitan ya fada cewar, gwamnati ta gayyato masu zuba jari domin aikin hako mai a arewacin Najeriyar.

Kachickwu ya kara da cewa, binciken da aka gudanar a watanni 6 da suka gabata, ya tabbatar da cewar, akwai albarkatun man fetur da iskar gas a shiyyar arewacin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China