in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta daina shigo da shinkafa daga ketare nan da 2018
2016-05-12 10:16:32 cri

Gwamnatin Najeriya za ta daina shigo da shinkafa da alkama, da sukari, da auduga da tuwon tumatir da nama daga kasashen ketare nan da shekarar 2018.

Ministar kasuwanci da masana'antu ta kasar Aisha Abubakar ta tabbatar da hakan yayin taron tattaunawa da masu zuba jari a lokacin taron koli game da tattalin arziki da zuba jari wanda aka gudanar a jihar Katsina dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Ta ce, Najeriya za ta daina sayo auduga da sauran kayayyakin 6 daga kasashen waje, domin samun dogaro da kanta wajen habaka masana'antun cikin gida don samar da tufafi a kasar.

Ministar ta ce, gwamnati mai ci tana da burin inganata masana'antu a Najeriyar don samar da kayayyakin da ake bukata a kasar.

Aisha ta ce, babu amfanin shigo da wadannan abubuwa 6 daga kasashen waje, tun da akwai su a cikin kasar.

Tun da farkon gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya bukaci masu zuba jari da su gabatar da tsare tsaren su domin kaucewa fuskantar duk wata matsala da za'a iya cin karo da ita game da batun zuba jari.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China