in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar tsaron Najeriya ta gargadi masu lalata bututun man kasar
2016-05-11 09:55:12 cri

Helkwatar hukumar tsaron Najeriya ta gargadi masu barnata kayayyakin kamfanonin man fetur da iskar gas na kasar a yankin Niger Delta mai albarkatun mai, ta bayyana cewar, za ta sanya kafar wando daya da dukkan daidaikun mutane ko kungiyoyi dake lalata kayayyakin samar da man fetur a kasar.

Kakakin hukumar tsaron kasar birgediya janar Rabe Abubakar ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta iske kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, inda hukumar tsaron kasar ta tabbatar da cewar, a shirye take ta dauki matakan kan dukkan masu barazanar kawo nakasu game ta ci gaban tattalin arzikin kasar.

Rabe ya ce, hukumar tsaron kasar tana sane da yunkurin da wasu kungiyoyin tsagerun yankin Niger Delta ke yi na durkusar da tattalin arzikin kasar ta hanyar fasa bututun man kasar, sai dai ya bayyana cewa, gwamnati ba za ta ragawa duk wani mutum dake yunkurin kawo nakasu game da sha'anin ci gaban tattalin arzikin kasar ba, kowane irin matsayi yake rike da shi.

Ya kara da cewar, hukumar tsaron Najeriya za ta dauki dukkan matakan da suka dace na murkushe kowane mutum ko kungiyoyin dake yunkurin lalata kayayyakin gwamnati a yankin Niger Delta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China