Wani jami'in ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Iraki ya bayyana cewa, wani bam da aka dasa cikin mota ya tashi a birnin Bagadaza, hedkwatar kasar, inda ya zuwa yanzu mutane a kalla 64 suka rasa rayukansu, yayin da wasu 87 suka jikkata. Kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS ta samar da daukar alhakin kai wannan harin. (Tasallah Yuan)