in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa dokar ta baci a babban birnin kasar Iraki
2016-05-01 13:39:17 cri

Jiya Asabar bangaren sojan kasar Iraki ya sanar da cewa, an kafa dokar ta baci a wannan rana a birnin Baghdad, sakamakon auka wa hukumomin gwamnati da jama'ar kasar suka yi.

A wata sanarwar da kakakin bangaren soja ya bayar an ce, an riga an rufe dukkan hanyoyin dake iya shiga Baghdad, ba a amince da shiga birnin ba, amma wadanda suke bukatar barin wurin, za su yi.

A yammacin Asabar, jama'a fiye da dubu sun auka wa "Green Zone" da muhimman hukumomin gwamnatin kasar suke, kana suka mamaye majalisar dokoki. Ya zuwa daren ranar kuma akwai jama'a da dama da suka taru a ginin majalisar dokokin. "Green Zone" wurin tsaro ne da aka kafa a cibiyar birnin Baghdad, wanda kuma akwai bukatar a nuna takardar musamman kafin shiga ko fita, ba a taba ganin irin lamarin na auka wa "Green Zone" da jama'a suka yi ba.

Bayan aukuwar lamarin, firaministan kasar Iraki Haider al-Abad shi ma ya bayar da sanarwa, inda ya yi kira ga jama'ar kasar da su janye jiki daga "Green Zone", kuma su koma wurin da aka tsaida don yin zanga-zanga, kana ya jaddada cewa, yanzu gwamnati ta maido da doka da oda a Baghdad.

A 'yan watannin da suka wuce, ana ta yin zanga-zanga don yaki da cin hanci da rashawa, da kuma bukatar yin garambawul ga gwamnatin kasar Iraki. A ranar 18 ga watan Maris, masu zanga-zanga fiye da dari sun zauna a kofar ta yankin "Green Zone", hakan ya samu goyon baya daga jam'iyyu da dama. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China