Wasu motoci biyu bakare da boma-bomai ne suka tarwatse a dab da wani ginin gwamnati dake birnin Samawah na jihar Liwa' Al muthanna, da kuma wani wurin ajiye motoci dake cibiyar birnin.
Rahotanni daga majiyar 'yan sandan wurin sun ce mai yiwuwa ne yawan mutanen da suka mutu a sakamakon tashin bama-baman zai ci gaba da karuwa.
Tuni dai kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin wannan hari, kungiyar da a baya ta sha kai makamantan wadannan hare hare a wurare daban daban na kasar Iraki.
Yanzu haka dai, kungiyar tana rike da ikon yawancin yammaci da arewacin kasar Iraki, kana suna musayar wuta tare da sojojin gwamnatin kasar a jihohi da dama.
Sojojin gwamnatin Iraki sun sanar da daukar matakan soji domin kwace ikon birnin Mosul cikin watan Maris, kafin daga bisani mayakan kungiyar ta IS su maida martani da manyan hare-hare. (Zainab)