Alkaluman baya-bayan da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Iraki ta fitar ya nuna cewa, baya ga wannan adadi akwai kuma mutane 117 da suka jikkata daga harin da aka kai kasuwar Mreidy da ke gundumar Sadar.
Maharan dai sun yi amfani da tsohon salo na kai hari ne, inda suka tayar da bam na farko domin su janyo hankalun jami'an tsaro da sauran jama'a, kafin daga bisani su tayar da bam na biyu, wanda ya yi mummunan barna.
Sa'o'i bayan tayar da wadannan bama-bamai ne, sai kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kaddamar da hare-hare. (Ibrahim Yaya)