in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai a kasar Iraki
2016-01-13 10:28:03 cri
Kwamitin sulhun MDD ya bayar da wata sanarwa a jiya, inda ya yi Allah wadai da harin ta'addanci da kungiyar IS ta kai birnin Bagadaza dake kasar Iraki, kana ya yi kira ga gwamnatin kasar Iraki da bangarori daban daban na kasar da su hada kai don yakar kungiyar IS ta yadda za a maido da zaman lafiya a kasar.

Sanarwar ta bayyana cewa, membobin kwamitin sulhun sun yi Allah wadai da dukkan hare-haren da kungiyar IS ta kaiwa jama'a a kasar Iraki , hare-haren da suka gurgunta kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin. Membobin kwamitin sulhun sun kuma jajantawa gwamnati da jama'ar kasar Iraki da kuma iyalan mutanen da suka mutu a sakamakon hare-haren da, tare da fatan mutanen da suka ji rauni za su samu sauki cikin hanzari.

Kwamitin sulhun ya kara da cewa, kamata ya yi kasashen duniya su martaba tsarin mulkin MDD, a kokarin da ake na yaki da ta'addanci da barazanar da hakan ke kawowa zaman lafiya a duniya. Kana membobin kwamitin sulhun sun bukaci kasa da kasa da su aiwatar da matakan yaki da ta'addanci bisa dokokin kasa da kasa, musamman dokokin 'yan gudun hijira da na jin kai ta duniya.

Rahotanni na cewa, ma'aikatar tsaron kasar Iraki ta bayyana cewa, samu fashewar wasu boma-bomai a birnin Bagadaza da jihar Diyala dake gabashin kasar a daren ranar 11 ga wata, wadanda suka haddasa mutuwar mutane a kalla 30, tare da raunatar mutane 71. Daga baya, kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai hare-haren. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China