in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 30 sun mutu sakamakon fashewar tagwayen boma-bomai a Iraki
2016-01-12 11:16:21 cri

Fashewar wasu tagwayen boma-bomai a daren jiya Litinin a jihar Diyala dake gabashin birnin Baghdad, babban birnin kasar Iraki, sun yi sanadiyyar hallaka rayukan mutane a kalla 30, a yayin da wasu 71 suka jikkata.

Wani jami'in majalisar harkokin cikin gida ta kasar Iraki ya bayyana cewa, maharan sun tada boma-boman ne da aka dasa cikin wata mota a gaban kofar wata kasuwar dake da yawan jama'a a gabashin birnin Baghdad a wannan rana, bugu da kari maharan sun sake tada wasu Karin boma-boman dake daure a jikinsu, kazal ika sauran maharan sun yi garkuwa da mutanen, sai dai an yi musayar wuta tsakanin maharan da sojoji da kuma 'yan sandan kasar.

Jami'in, ya tabbatar da cewa, bayan shafe wasu sa'oi ana gumurzu, sojoji sun yi nasarar kwace wannan kasuwa, kuma sun hallaka wasu daga cikin maharan, kuma an bada labarin rasuwar mutane a kalla 7, yayin da wasu mutane 27 suka jikkata, kuma an saki dukkan mutanen da maharan suka yi garkuwa da su.

Daga bisani, kungiyar IS ta sanar da cewa, ita ce ke da alhakin kai wannan harin. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China