Wata majiya daga ofishin ministan harkokin cikin gidan kasar ta shedawa kamfanin dillanin labaran kasar Sin Xinhua cewar, harin an kaddamar da shi ne a kasuwar Mreidy dake unguwar Sadr.
Majiyar ta kara da cewar, yan kunar bakin wake sun tada bomai bomai da ke jikinsu ne a kasuwar wacce ke da cunkoson jama'a kuma galibin jama'ar dake taruwa mabiya shi'a ne.
Fashewar tayi sanadiyyar lalata shaguna da dama dake kusa da inda abin ya faru, kuma motoci da dama sun kama da wuta.
Maharan dai sun yi amfani ne da wani salo, inda suka tada bam na farko don a samu taruwar jami'an tsaro da sauran jama'a, yayin da suka tada bam na biyu wanda ya haddasa mummunar barna.
A halin yanzu, Iraqi na fuskantar tashe tashen hankula, tun bayan da kungiyar IS mai da'awar kafa daular Islama ta kame wasu yankuna da dama a arewaci da yammacin kasar a watan Yunin shekarar 2014.
Tun da farko rahoton MDD ya nuna cewar, sama da mutane dubu 22,300 ne aka kashe a Iraqi a shekarar 2015.(Saminu Alhassan)