in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin "ziri daya da hanya daya" na biyan bukatun shirin raya kasa na kasashen da shirin ya shafa
2016-05-11 20:48:11 cri

Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, dalilin da ya sa shirin nan na "ziri daya da hanya daya" ya samu karbuwa sosai cikin gajeren lokaci shi ne shirin yana biyan bukatun kasashen duniya na samun zaman lafiya da bunkasuwa, musamman ma kasashen da shirin ya shafa, haka kuma yana dacewa da moriyar bai daya ta kasashen da shirin ya shafa ta fuskar yin hadin gwiwa.

Lu Kang ya fadi haka ne a yau Laraba yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, ya kuma kara da cewa, bisa ka'idar yin tattaunawa tare da raya shirin tare da kuma cin gajiyar shirin tare, kasar Sin za ta ci gaba da kyautata manufofinta na raya kasa ta yadda za su dace da kasashe da kungiyoyi masu ruwa da tsaki na duniya, zurfafa hadin gwiwa a sassa daban daban, a kokarin kawo alheri ga daukacin al'ummar kasashen duniya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China