in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Ogun a Najeriya na bukatar karin masu zuba jari daga Sin
2016-05-05 09:06:39 cri

Mahukuntan jihar Ogun dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya sun bayyana cewar, jihar na bukatar karin masu zuba jari daga kasar Sin, don gudanar da wasu ayyukan ci gaban jihar.

Kwamishinan kasafin kudi da tsare tsare na jihar Aderenle Adesina, ita ce ta tabbatar da hakan gabannin taron dandalin zuba jari wanda ake sa ran gudanarwa a ranakun 10 da 11 ga watan Mayu a Abeokuta, babban birnin jihar ta Ogun.

Adesina ta ce, gwamnatin jihar tana bukatar gayyato karin masu zuba jari daga kasar Sin domin samar da kudaden gudanar da muhimman ayyukan more rayuwa a jihar, inda ta bayyana cewar, za'a yi amfani da dandalin ne a matsayin wata hanyar sadarwa tsakanin gwamnatin jihar da masu zuba jarin.

Ta ce, kimanin kamfanoni 100 ne suka kulla huldar kasuwanci da jihar ta Ogun tun bayan kaddamar da dandalin a shekarar 2012.

Gwamnan jihar Ogun Idikunle Amosun, na daga cikin wakilan da suka rufawa shugaba Muhammad Buhuri na Najeriya baya a ziyararsa zuwa kasar Sin a watan Aprilu, shi ma yana daga cikin mahalarta taron dandalin tattaunawar cinikayya tsakanin Najeriya da kasar Sin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China