in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kamaru yana ziyara a Najeriya
2016-05-04 09:31:20 cri

A jiya Talata ce shugaba Paul Biya na kasar Kamaru ya isa Najeriya don gudanar da wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu bisa gayyatar takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari.

A yayin ziyarar, ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna kan batutuwa da suka shafi muradun kasashensu, ciki har da hadin gwiwar da kasashen yankin ke yi game da yaki da ayyukan ta'addanci, tsattsauran ra'ayi, da sauran manyan lafuffukan da ake aikatawa a kan iyakokin kasashen.

Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar ta nuna cewa, shugaba Biya zai karkare ziyarar tasa da sanya hannu kan sabbin yarjejeniyoyin hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Najeriya da kasar ta Kamaru.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, za a fitar da sanarwar bayan taro ta hadin gwiwa game da abubuwan da shugabannin kasashen biyu da jami'ansu suka tattauna yayin ziyarar kafin shugaba Biya ya bar Abuja a yau Laraba.

Shugaba Buhari ne dai ya tarbi takwaran nasa tare da manyan jami'an gwamnatin kasar ta Kamaru da suka rufa masa baya yayin wannan ziyara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China