in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani kamfanin kasar Sin na taimaka wa Djibouti shimfida tagwayen hanyoyin mota
2015-06-17 10:46:00 cri

A ranar 15 ga wata ne, aka shirya bikin kaddamar da aikin shimfida tagwayen hanyoyin mota a birnin Djibouti, hedkwatar mulkin kasar Djibouti, wanda kamfanin shimfida hanyoyin zirga-zirga na kasar Sin ya samu kwangila. Hanyar mota da za a shimfida har zuwa iyakar kasar Habasha ta kasance hanyar mota mai saurin tafiya ta farko a kasar Djibouti.

Shugaban kasar Ismail Omar Guelleh ya bayyana a yayin bikin, imaninsa cewa, tabbas ne za a kammala wannan aiki yadda ya kamata, hanyar kuwa za ta taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin kasashen Djibouti da Habasha, har ma da dinkuwar duk shiyyar da kasashen biyu ke ciki.

A nasa bangaren, Sun Ziyu, mataimakin babban manajan wannan kamfanin kasar Sin ya yi tsokacin cewa, kamfaninsa zai yi namijin kokari domin kammala aikin shimfida wannan hanyar mota yadda ya kamata, a kokarin ba da gudummawarsa wajen inganta hadin gwiwar kasashen Sin da Djibouti a fannin tattalin arziki da kuma kara dankon zumunci a tsakaninsu.

An labarta cewa, tsawon wannan hanyar mota mai saurin tafiya ya kai kilomita 77, wadda za ta ba da sauki ga harkokin sufuri a tsakanin Djibouti da Habasha, baya ga samar wa Djibouti dubun dubantar guraben ayyukan yi.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China