A yayin ganawar tasu, shugaba Guelleh ya bayyana cewa, cikin 'yan shekarun nan, kasashen biyu sun samu ci gaba bisa hadin gwiwarsu a fannonin siyasa, tattalin arziki, tsaro da sauransu, haka kuma, kasarsa na godiya ga fahimta da goyon baya da kasar Sin ta baiwa kasarsa, yana fatan iri wannan zumunci zai ci gaba da kasancewa a tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangaren kuma, janar Fang Fenghui ya ce, kasar Sin na fatan ci gaba da yin shawarwari da shugabannin kasar Djibouti, domin karfafa fahimtar juna da hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu. (Maryam)