in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Djibouti suna tattaunawa kan gina ababen ba da tabbaci ga ayyukan kiyaye zaman lafiya
2015-11-26 20:13:21 cri

Rahotanni na cewa, kwamandan hedkwatar rundunar sojan kasar Amurka a nahiyar Afirka David M. Rodriguez ya ce, kasar Sin ta yi shirin gina wani sansanin soja a kasar Djibouti, wanda ya kasance sansanin soja na farko da Sin ta gina a nahiyar Afirka.

Dangane da haka, Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau a yayin taron manema labaru a nan Beijing cewa, akwai kyakkyawar hulda a tsakanin Sin da Djibouti, suna tattauna kan gina wata tashar da sojojin Sin za su rika yada zango a Djibouti, lamarin da zai taimakawa sojojin kasar Sin a ayyukan da suke yi na kiyaye zaman lafiya a duniya, ba da kariya ga zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin tekun Aden da yankin teku na Somaliya, ba da agajin jin kai da dai sauransu, matakin da zai taimakawa sojojin Sin wajen sauke nauyin da kasashen duniya suka dora musu yadda ya kamata, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da shiyya-shiyya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China