Hukumar rage radadin bala'i ta kasar ta bayyana cewa, ban da wajen filin jirgin sama Tacloban da ke fama da bala'in sosai, ya zuwa yanzu an maido da zirga-zirga a dukkan filayen jiragen sama na jama'a. Haka kuma, ma'aikata masu aikin ceto suna kokarin warware batun samar da wutar lantarki da farfado da harkokin sadarwa. Haka kuma, masu shagunan sadarwa dake birnin Tacloban sun baiwa mutane damar buga waya kyauta domin su tuntubi 'yan uwansu. Amma, sakamakon lalacewar layoyin da turakan samar da wutar lantarki, yanzu, akwai yankuna da dama da ba su da hasken wutar lantarki.
A sa'i daya kuma, wasu kasashen da suka aike da ma'aikatan jinya da sun isa wuraren da ke fama da mahaukaciyar guguwar ta Haiyan sosai, don ba da taimakon jinya.(Bako)