Bisa wannan rahoto, an ce, bayan mako guda da abkuwar bala'in, yawan mutanen da suka mutu yana karuwa a wurare daban daban na Philippines.
Ban da haka, kwamitin rage yawan bala'u na kasar ya bayyana cewa, kawo yanzu mutane sama da dubu 18 daga gwamnatoci na mataki-mataki da kungiyoyin masu aikin sa kai suna aikin ceto, tare da motoci 844, da jiragen ruwa 44, da kuma jiragen sama 31.(Fatima)