Da ma dai sakamakon matsalar tabarbarewar tsaro a kasar, ofishin jakadancin ya daina aiki tun a watan Janairun shekarar 2013, yayin da aka tura wasu ma'aikatan ofishin zuwa birnin Damascus, hedkwatar kasar. Kawo yanzu dai, wasu ma'aikata 'yan Syria ne kadai ke cigaba da gudanar da aikinsu a ofishin.
A jiya Juma'a, kamfanin dillancin labaru na Syria ya ba da labarin cewa, birnin Aleppo dake arewacin kasar ya sake fuskantar luguden wuta. Wannan ne rana ta 7 a jere, da ake kaddamar da hari a birnin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 100.
A ranar 28 ga wata, yayin da ministan watsa labaru na Syria, Omran Zoabi ya yi magana da wakilin gidan talebijin din kasar, ya bayyana cewa, jerin hare haren da ake kaiwa birnin Aleppo a kwanan baya tamkanr laifin yaki ne, wanda a cewarsa, ya zama dole gwamnatin Syria da sojoji su mai da martani.
Birnin Aleppo ya taba zama cibiyar tattalin arzikin kasar Syria, kuma birni mafi girma a kasar. Yanzu sojojin kasar da dakaru masu adawa da gwamnatin kasar da kuma kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi sun mamaye wurare daban daban na wannan birni.(Fatima)