An bayyana cewar, reshen kungiyar al-Qaida dake kasar Syria na Al-Nusra ya kai hare-haren kan wasu ungwannin fararen hulda dake birnin Aleppo, wadanda suka fara daga ranar 29 har zuwa ranar 30 ga wata.
Bayan da kasashen Amurka da Rasha suka cimma yarjejeniya don ganin bangarorin da ba sa ga maciji da juna a kasar Syria su tsagaita bude wuta a ranar 22 ga watan Fabrairun bana, an samu sassauci game da yanayin tsaro a wannan kasar. Sai dai a 'yan kwanakin baya, yanayin kasar ya sake tsanantawa, sakamakon janye jiki na wasu kungiyoyin masu adawa da gwamnati daga cikin yarjejeniyar.(Bello Wang)