in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afrika ta Kudu ya sha alwashin daukan matakin dakile zanga zanga na tashin hankali
2015-12-10 10:28:09 cri
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma a ranar Laraban nan ya ce, zai dauki mataki mai karfi domin dakile duk wani zanga zanga na tashin hankali da lalata kayayyaki da yanzu yake kunno kai.

Ya ce, babban matakin da gwamnati za ta dauka shi ne da zai bukaci karin nazari domin daman tun farko ana bincike a kan hakan.

Mr Zuma ya yi wannan bayanin ne a martanin da ya mayar wa tambayar da majalissar dokokin kasar ta yi mashi ko yana da niyyar samar da wani bincike ta kimiyya da zai bayyana dalilin da ya sa 'yan kasar yanzu suke fara tashin hankali, ko sace sace da lalata kayayyaki idan suna aiwatar da zanga zanga.

Karuwan tashin hankalin da aka yi yana komawa fagen sace sace da lalata kayayyaki ya zama abin damuwa kwarai, in ji Mr Zuma.

Tashin hankali yanzu a cikin al'umma ya samo asali ne tun daga wanda aka yi lokacin nuna kyamar wariyar launin fata kuma yadda aka yi a lokacin ba kamar sa.

Ya ce, akwai binciken da ake yi domin fahimtar dalilan dake haddasa al'adun tashin hankali a cikin al'umma. Wassu binciken ma kungiyoyin da ba na gwamnati ba ne ke yin su.

Shugaban na kasar Afrika ta Kudu daga nan sai ya tabbatar da cewa, gwamnati za ta dauki matakai masu yawa da muhimmanci domin shawo kan wannan lamari a shekara mai kamawa, wadanda suka hada da ilimantar da jama'a game da 'yancin da nauyin da ke wuyansu a matsayin 'yan kasa.

Shirin ilimantarwan yana da muhimmanci kwarai ganin cewa shekara mai zuwa za'a cika shekaru 20 cif na rattaba hannu a kan kundin tsarin mulkin kasar da marigayi tsohon shugaba Nelson Mandela ya yi. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China