Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin kasar Amurka 150 sun riga sun kutsa kai cikin yankin Rumailan na kasar ta Syria, wanda tuni Syria ta nuna damuwa game da hakan. A ganin mahukuntan kasar, hakan ya kawo barazana duba da yadda sojojin suka shiga yankin ba tare da samun izni ba, kana hakan ya keta ikon mulkin kai na kasar Syria. Don haka kasar Syria ta yi Allah wadai da shi.
Sanarwar ta bayyana cewa, tura sojoji zuwa Syria da Amurka ta yi ba ya bisa doka, kuma kasar ba za ta amince da hakan ba. Kaza lika ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakai na dakatar da wannan aiki, wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya sanar da tura sojoji 250 zuwa kasar Syria a ranar 25 ga watan nan. A cewarsa, an dau wannan mataki ne domin taimakawa dakaru masu adawa da gwamnati dake da sassaucin ra'ayi a kasar ta Syria wajen yaki da kungiyar IS.
Ya zuwa karshen shekarar 2015, gwamnatin kasar Amurka ta riga ta tura sojojin musamman 50 zuwa kasar Syria. (Zainab)