A yayin taron manema labarai da aka yi a wannan rana, Mr. Mistura ya ce, ana fuskantar kalubalen kawo karshen yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka fara aiwatarwa a ranar 27 ga watan Fabrairu na shekarar bana, don haka, ya yi kira ga kasashen da abin ya shafa da gamayyar kasa da kasa da su ba da karin gudummawa kan wannan aiki, domin ganin dorewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Syria, wanda bangarorin da abin ya shafa suka dukufa matuka domin samun wannan nasara, a sa'i daya kuma, ya bukaci da a kira taron ministocin mambobin kasashen tawagar dake goyon bayan Syria cikin sauri, domin ciyar da shawarwarin neman sulhu na mataki mai zuwa gaba da kuma samun sakamakon da gamayyar kasa da kasa suke sa ran cimmawa.
Bugu da kari, Mr. Mistura yana fatan bayyana ranar gudanar da taron shawarwarin neman sulhu kan batun Syria na mataki mai zuwa a watan Mayu mai zuwa. (Maryam)