A karo na uku, an sake mayarwa majalissar dokokin Najeriya kundin kasafin kudin kasar na wannan shekara, bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya duba shi, ya kuma bukaci a sake yiwa kundin wasu sauye sauye. Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban na Najeriya ya amshi kundin kasafin kudin da safiyar yau Laraba, amma kuma aka mayarwa zauren majalissar shi da tsakar rana, domin su sauya wasu sassa da tsagin zartaswar bai gamsu da su ba.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta cire kwamishinan 'yan sandan jihar Enugu Nwodibo Ekechukwu daga mukamin sa, sakamakon harin da ake zargin wasu Fulani makiyaya da kaddamarwa kan al'ummar yankin Ukpabi Nimbo dake jihar ta Enugu. Jami'in hulda da jama'a na rundunar Bisi Kolawole, ya tabbatar da hakan ga manema labarai, yana mai cewa tuni aka sauyawa Ekechukwu jihar aiki.
Alamu na nuna cewa gwamnonin wasu jihohin Najeriya na ci gaba da kashe makudan kudade wajen tafiye tafiye zuwa kasashen waje, bisa dalilai da suke dangantawa da nemowa jihohin na su masu zuba jari, duk kuwa da kanfar kudade da ake kukan na addabar jahohin.
Wasu masu sharhi na ganin duk da faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya, da kuma rashin isassun kudaden shiga, wasu daga gwamnonin Najeriyar basu rage irin kudin da suke kashewa wajen tafiyar da jihohin su ba.(Saminu Alhassan)