Gwamna El-Rufa'i, wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar, yayin wani taron jin ta bakin al'umma, ya ce a baya bayan nan an samu ci gaba matuka a fannin ingantuwar tsaro, tare da raguwar yawan kisan kai da satar shanu, laifukan da a baya suka addabi jihar.
Ya ce ga dukkan alamu masu aikata irin wadannan laifuka sun karkata ga yin garkuwa da mutane, sai dai duk da hakan jami'an rundunar 'yan sandan jihar na samun nasara kan miyagun dake aikata manyan laifuka a jihar.
Gwamnan ya kara da cewa, a 'yan kwanakin nan rundunar 'yan sandan jihar ta cafke wani jigo a wani gungu na masu satar mutane, inda aka samu tarin makamai daga maboyar wadannan miyagu.(Saminu Alhassan)