Gwamnan ya kara da cewa, ziyarar da shugaban ya yi a kasar Sin, ta sa bangarorin 2 sun kulla yarjeniyoyi daban daban da suka shafi aikin samar da wutar lantarki, da hakar ma'adinai, da zirga-zirgar motoci, da aikin gona, da dai makamantansu. A cewar gwamnan, hakan zai ciyar da tattalin arzikin kasar gaba, gami da amfana wa daukacin al'ummar kasar.
A bangaren jihar Legas kuwa, in ji gwamnan, ta samu moriya sosai bisa manyan ayyukan da aka kulla tsakanin Najeriya da Sin, wadanda suka hada da gina layin dogo na karamin jirgin kasa wanda zai shafe dalar Amurka biliyan 2.5, gami da babban layin dogon da zai hada jihar Legas da ta Kano.(Bello Wang)