Buhari, ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, a loakcin tattaunawa da ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian, a Abuja fadar mulkin kasar.
Ya ce kasarsa za ta cigaba da tsaurara matakan tsaro a yankin, domin samar da ingantaccen tsaro, da kuma dakile aniyar masu satar danyen mai da masu fashin jirgin ruwa.
Da ma dai akwai dakarun tsaro na kawance daga kasashen Najeriyar, da Chadi, da Kamaru, da Nijer da kuma jamuhuiriyar Benin, wadanda ke yaki da mayakan Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar.
Ya ce a halin yanzu dakarun Najeriyar suna cigaba da yin lugudan wuta kan mayakan a dajin Sambisa.
Shugaba Buhari, ya lashi takobin murkushe mayakan na Boko Haram, wadanda suka hallaka mutane sama da 10,000, tun bayan kaddamar da hare hare a shekarar 2009. (Ahmad Fagam)