in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya na kaddamar da hare-hare a mafakar Boko Haram
2016-05-02 12:19:02 cri
Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kaddamar da manyan hare-hare a dajin Sambisa dake jihar Borno, a wani mataki na fatattakar dakarun Boko Haram daga maboyar dake wannan daji.

Manjo janar Lucky Irabor, wanda shi ne babban kwamanda mai kula da aikin soja na musamman da aka yiwa lakabin Lafiya Dole, ya bayyana hakan a jiya Lahadi, yayin zantawar sa da manema labaru a birnin Maiduguri, hedkwatar jihar Borno.

A cewar hafsan, a halin yanzu sojojin kasar karkashin jagorancin birgadiyar janar Victor Ezugwu, na tsakiyar dajin Sambisa inda suke kaddamar da hare-hare kan sansanoni da wuraren buyar 'yan Boko Haram, kuma tuni suka cimma manyan nasarori a 'yan kwanakin baya bayan nan. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China