Ministan harkokin waje na Sin Wang Yi wanda ya jagoranci taron ya kuma gabatar da jawabi.
Wang Yi ya ce, tun bayan da ya hau kujerar shugabancin taron CICA a shekarar 2014, Sin tana martaba ra'ayin tsaro na yankin Asiya tare da yin hadin gwiwa tsakaninsu da kuma sauran membobin taron. Wang ya kuma jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da bin manufofin diplomasiya da shugaba Xi Jinping ya gabatar da ra'ayin tsaro na Asiya, domin karfafa hadin gwiwa da amincewa da juna tsakaninta da bangarori daban daban, da zurfafa hadin gwiwa a duk fannoni, ta yadda za a bude wani sabon babi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun ci gaba gami da walwala a yankin Asiya da ma duniya baki daya.(Fatima)