in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin Xi Jinping kan tsaro a shiyyar Asiya ya jawo hankalin duniya
2014-05-22 15:56:26 cri

An kira taro na matakin farko kan batun inganta cudanya da karfafa hadin gwiwa a nahiyar Asiya na CICA a ranar Alhamis 21 ga wata a birnin Shanghai na kasar Sin a karkashin jagorancin shugaban kasar Xi Jinping. A cikin jawabin da ya gabatar, Xi ya tabo batun tsaro a shiyyar Asiya, da kuma yadda za a samu ci gaba da nasara tare da kuma yadda za a amfana da sakamakon da ake samu a wannan fanni.

Jawabin shugaba Xi ya jawo hankalin kafofin watsa labarai na kasa da kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Rasha ya ba da labari a ranar 21 ga wata, cewar shugaba Xi ya yi kira da a tsara da kuma cimma daidaito kan wani salon ra'ayin tsaro guda da zai iyar taimakawa yin hakuri da juna. Rahoton ya kuma jaddada cewa, ma'anar tabbatar da tsaro baki daya ita ce girmama juna da samun zaman lafiya a ko wace kasa.

Haka kuma kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ba da labari a wannan rana, cewar shugaba Xi ya nuna cewa, kulla kawancen sojoji don nuna gaba ga ragowar kasashe ba zai ba da taimako wajen kiyaye tsaron lafiya na shiyya-shiyya ba. Game da wannan, sharhin ya cigaba da cewa, Xi na fatan kawar da damuwar da kasashe suke nunawa kan kasar Sin a cikin jawabin nasa tare da jaddada cewa, ko da yaushe kasar Sin ta kan nuna himma da kwazo wajen warware matsalolin da suka shafi ikon mallakar yankunan kasa da muradun teku cikin ruwan sanyi.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China