Ya kuma kara da cewa, jawabin ya bayyana halin da nahiyar Asiya ke ciki a halin yanzu, kuma ya jaddada aniyar kasar Sin wajen yin hadin gwiwa da bangarorin daban daban da abin ya shafa don wanzar da tsaron nahiyar bisa muhimman fannoni cikin hadin gwiwa da kuma cikin dogon lokaci, ta yadda za a iya ciyar da sabon tsarin tsaron nahiyar gaba bisa tattaunawar da aka yi a yayin taron CICA, hakan zai taimaka a kiyaye tsaron nahiyar ta hanyoyin hadin gwiwa da cin moriyar juna. (Maryam)