Mr. Cheng ya bayyana hakan ne yayin taron maneman labaru na gida da na ketare, wanda aka gudanar a cibiyar yada labaran babban taron na CICA dake birnin Shanghai na kasar Sin a Lahadin nan.
Har ila yau Mr. Cheng ya kara da cewa, wakilan mambobin babban taron na CICA, wadanda suka hada da shugabannin kasa da kasa, da na wasu kungiyoyin kasashen duniya za su halarci taron nan, ciki hadda shugabannin kasashen duniya 11, daga kasashen Afghanistan, Iran, Rasha, Kazakhstan da dai sauransu, baya ga wasu shugabannin kungiyoyin kasashen duniya 10, da suka hada da babban magatakardar MDD Ban Ki-moon.
Haka zalika, ministan harkokin wajen kasar Turkiya Ahmet Davutoglu zai halarci taron a matsayin wakilin musamman na shugaban kasar Abdullah Gul.
Bugu da kari, Mr. Cheng ya ce a yayin taron na wannan karo, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gana da shugabannin kasashen Rasha, da Kazakhstan, da Kyrgyzstan da kuma Iran. (Maryam)