Yau Alhamis ne aka kaddamar da taron ministoci karo na 5, na taron inganta hadin kai da amincewar kasashen Asiya na CICA a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron, gami da gabatar da jawabi mai taken "Cimma matsaya guda da sa kaimi ga gudanar da shawarwari, don kago makoma mai haske ta raya zaman lafiya da wadata a kasashen Asiya. A cikin jawabin nasa, ya jaddada cewa ya kamata a nace kan manufar tsaro bai daya cikin dogon lokaci, da cimma matsaya guda, kana da sa kaimi ga yin shawarwari, da inganta hadin gwiwa, domin raya salon tsaron da ke da halin musamman na kasashen Asiya. Ta hakan ne za a raya makoma mai haske wajen samar da zaman lafiya da wadata a Asiya.
Cikin manyan baki a taron hadda mamban majalisar gudanarwar Sin Yang Jiechi, da kuma ministan harkokin wajen Sin Wang Yi wanda shi ne ya shugabanci taron.
An bude taron na yini biyu ne dai jiya Laraba, za kuma a kammala shi yau Alhamis, inda mambobin kasashen CICA, da masu sa ido, da sauran kungiyoyi sama da 40 suka kasance cikin mahalartan sa. (Bako)