Mr Schlettwein ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi, yayin kaddamar da taron fidda rahoto, game da harkokin jagoranci a nahiyar Afirka karo na 4 a birnin Addis Ababan kasar Habasha.
Ministan ya kara da cewa cin hanci da rashawa ya kai matakin koli a nahiyar Afirka, musamman ma a kasahen dake fama da yake-yake, da masu tarin arzikin ma'adanai.
Rahoton da aka gabatar dai na kunshe da awon mizanin ayyukan cin hanci da rashawa, yana kuma haskaka matsayin wannan matsala, da tasirin ta ga huldar kasa da kasa.
An kaddamar da rahoton ne dai yayin bikin makon ci gaban nahiyar Afirka, wanda kungiyar ECOWAS da AU suka shirya, zai kuma gudana tsakanin ranekun 31 ga watan Maris zuwa 5 ga watan nan na Afirilu.