in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar yaki da ta'addanci ta kasashen musulmai ta tsara shirin daukar matakai
2016-03-28 14:53:18 cri
A jiya Lahadi 27 ga wata, hadaddiyar kungiyar yaki da ta'addanci na kasashen musulmai da kasar Saudiya ta kafa, ta kira taron koli a karo na farko a birnin Riyadh, hedkwatar kasar Saudiya, domin tsara shirin daukar matakan yaki da ta'addanci a nan gaba.

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Saudiya, Brig. Gen. Ahmed Assiri ya bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya bayan taron cewa, kungiyar za ta yi kokarin yaki da kungiyoyin ta'ddanci, ciki har da kungiyar IS daga fannoni hudu, wato aikin soja, nazari, kudi, da kuma fadakarwa.

Manyan kwamandoji da sauransu daga kasashe 39 sun halarci wannan taro na yini guda, ciki har da Masar, Turkiya, daular kasashen larabawa, Malaysiya, Pakistan, da ma wasu kasashen Afirka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China