A bisa tsarin wannan shiri, za a fadada kwarewar jihar Tibet a fannin aikin ban ruwa, da tsimin ruwa, da gina karin kayayyakin adana ruwa a kauyukan jihar, da kyautata fasahohin jihar a fannin magance bala'i, da kiyaye muhalli a yankunan dake daf da tabkuna da koguna, da gyare-gyaren tsarin aikin adana ruwa nan da shekarar 2020.
Ministan aikin adana ruwa na kasar Sin Chen Lei, ya bayyanawa mahalarta taron da aka kira a ranar Lahadi cewa, jihar Tibet ta kasance mafarin manyan kogunan kasar Sin, da yankin adana ruwa na kasar, tana kuma da wani matsayi mai muhimmancin gaske a fannin tsaron muhalli a kasar. Don haka a cewar sa tilas ne a yi kokarin fidda manyan tsare-tsare masu nagarta, ta yadda za a samu daidaito tsakanin cin gajiyar albarkatun ruwa, da kuma kokarin tsimin sa. (Bello Wang)