Jihar Tibet mai cin gashin kanta dake kudu maso yammacin kasar Sin na shirin kara matsakaicin adadin tsawon rayuwar mazauna jihar, da shekaru biyu, domin cimma matsayin shekaru 70 nan da shekaru biyar masu zuwa, in ji Zeng Wanming, shugaban sashen kula da raya jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da horar da kwararru da mambobin jam'iyyar ta jihar, a yayin wani taron da ya shafi bangaren kiwon lafiya na Tibet, tare da bayyana cewa, ma'aikatun kiwon lafiya za su kara kyautata da fadada aikinsu domin cimma wannan buri.
Matsakaicin adadin tsawon rayuwa a Tibet ya kasance da shekaru 68.2 a shekarar 2013, wanda ya karu idan aka kwatanta da shekaru 35.5 kafin samun 'yancin jihar cikin lumana a shekarar 1951. Amma duk da haka ya yi kasa da shekaru 8 idan aka kwatanta bisa ga na kasa baki daya, dalilin matsayin jihar dake kan tudu da kuma matsalolin samun ayyukan kiwon lafiya a wannan jiha da ba ta da yawan mutane.
A wannan jihar dake kan tsaunuka, wata karamar mura na iyar kasancewa ajali ga wani mai nakasa, in ji Tashi, wani likita na kauyen Tsewugarmo, dake hukumar Ngari, inda ya kara da cewa, kafin zuwan malaman kiwon lafiya na kamfe, yawancin 'yan Tibet dake karkara sai sun yi tafiyar kilomita da dama domin su ga lilkita.
Ko wane kauye na Tibet na da a halin yanzu asibiti dake da a kalla likita biyu, sakamakon taimakon kudi na Yuan biliyan hudu kwatankwacin dalar Amurka miliyan 627 da gwamnatin tsakiya ta samar a shekaru biyar da suke gabata. (Maman Ada)