Dole ne a kokarta samun babban ci gaba a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma a jihar Tibet cikin dogon lokaci
Shugaban majalissar bada shawara kan harkokin siyasar kasar Sin Yu Zhengsheng, ya jaddada cewa yanzu abin dake gaban komai shi ne shugabannin al'ummomin jihar Tibet su tabbatar da aiwatar da ra'ayin taron karawa juna sani kan harkokin jihar Tibet karo na 6, wanda ya bayyana kalaman shugaban kasar Sin Xi Jinping, bisa tsarin "Yayin da ake kulawa da kasa, wanda ya nuna cewa dole ne a kula da yankunan iyakar kasa tukuna, kuma yayin da ake kulawa da yankunan iyakar kasa, dole ne a kula da jihar Tibet tukuna". Shugaba Xi ya nuna cewa hakan zai taimaka wajen kokarin tabbatar da kwanciyar hankali, da samun babban ci gaba a fannonin tattalin arziki, da ma zamantakewar al'umma a jihar cikin dogon lokaci.
Mr. Yu ya bayyana hakan ne a Talatar nan a birnin Lhasa, yayin da yake sauraron rahoton aikin kwamitin JKS na jihar Tibet mai cin gashin kanta, da na gwamnatin jihar. (Fatima)