A cikin wannan bidiyo na "soke tsarin bayi", an bayyana wa 'yan kallo wannan muhimmin matakin soke tsarin bayi a yankin Tibet da aka dauka a tarihin ci gaban dan Adam a karni na 20 da ya gabata. Sannan kuma, an bayyana tarihin tsarin bayi, da yadda aka keta da zalunta ikon bayi a yankin Tibet. Bugu da kari kuma, an bayyana muhimmancin soke tsarin bayi a yankin Tibet ga mutanen da suke zaune a yankin da kokarin ci gaban 'yancin dan Adam a duk duniya gaba daya. Haka kuma, an bayyana ci gaban da aka samu a sabuwar jihar Tibet mai cin gashin kanta a cikin wadannan shekaru 57 da suka gabata.
An bayyana cewa, a lokacin da ake daukar wadannan bidiyo biyu, an yi amfani da tarin bayanan tarihi na bidiyo kan yadda aka soke wannan tsarin bayi a yankin Tibet a shekarar 1959. Bugu da kari kuma, an kai ziyara ga wadanda suka taba yin wannan aiki da masanan gida da na waje wadanda suke nazarin wannan batu, a kokarin mayar da ainihin tarihin soke tsarin bayi a yankin Tibet daga bangarori daban daban, da kuma an gane cewa wannan ya zama wajibi da aka soke tsarin, har ma za a iya tunanin muhimmancin matakin soke shi wajen 'yantar da kuma mutunta hakkin dan Adam. (Sanusi Chen)