in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanayin halittun tsaunin Tibet na samun kyautatuwa, in ji rahoton kwalejin binciken kimiyya ta Sin
2015-11-18 13:42:45 cri

Cibiyar kula da tsaunin Qinghai-Tibet ta kwalejin binciken kimiyya ta kasar Sin ta bayar da wani rahoto a yau Laraba cewa, yanayin halittun da ke tsaunin Tibet na samun kyautatuwa. Rahoton da masana kimiyya na gida da na waje suka rubuta ya kasance rahoto na farko da ke nazarin kan yanayin tsaunin Tibet daga dukkan fannoni a kimiyance

Rahoton ya yi bayani game da yanayin halittu da ke tsaunin na Tibet tun daga shekaru 2000 da suka wuce har zuwa shekaru 100 masu zuwa, ta hanyar amfani da ma'aunai 26 kamar su awon yanayi, yawan ruwan sama, dutsen kankara, kankara mai laushi, tabkuna, wadanda suke cikin fannoni shida, kamar su yanayi, tsarin ruwa, na'u'o'in halittu, muhallin doron kasa, harkokin dan Adam, kana da bala'i daga indallahi.

A cikin nazarin masana kimiyya sun gano cewa, yanayin halittu na yankin Tibet ya samu kyautatuwa, yayin da ake kiyaye ire-iren halittu yadda ya kamata. Bugu da kari, akwai albarkatun ma'addinai a wurin, wadanda za a iya hako su a nan gaba.

Don haka rahoton ya ba da shawarar cewa, ya kamata a yi amfani da bayanan kimiyya wajen kiyaye muhallin halittu da raya ayyukan tattalin arziki marasa gurbata muhalli tare, baya ga sanya gwamnati a cikin wannan aiki. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China