Alamu na nuna cewa, 'yan majalissun dokokin Najeriya na fatan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari, domin warware bambance-bambancen dake tsakanin sashen zartaswa, da na dokoki game da kasafin kudin kasar na bana. Wasu jaridun kasar sun ruwaito cewa, sassan majalissun biyu sun jingine batun sake duba kasafin kudin har sai bayan ganawarsu da shugaban kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sake rokon 'yan kasarsa da su kara hakuri da juriya, bisa mawuyacin halin matsayi da ake fuskanta a kasar. Shugaba Buhari ya ce, saura kiris 'yan kasar su fara shan romon mulkinsa. Buhari ya kara da cewa, canjin da 'yan kasar suka zaba sannu a hankali zai karade dukkanin sassan kasar.
Wasu rahotanni na cewa, duk da kudaden tallafin fita daga matsi da gwamnatin tarayyar Najeriya ta samar ga jahohi, akwai jahohin da har yanzu ma'aikata ke bin gwamnatocin su bashin albashi daga wata guda zuwa watanni 9.
Karancin kudaden canji na dalar Amurka a Najeriya alheri ne ga kasar, duba da yadda tuni hakan ya sanya kananan masana'antun kasar fara farfadowa cikin sauri. Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan a jihar Kebbi, lokacin da ya ziyarci gonakin noma dake jihar wadanda bankin ya samarwa tallafi. (Saminu Alhassan)