Ministan harkokin sufuri a tarayyar Najeriya Rotimi Amechi, ya ce gwamnatin kasar mai ci na daukar karin matakai na inganta harkokin sufuri, lamarin da a cewarsa, zai yi matukar bunkasa fannin cinikayya tsakanin al'ummar kasar.
Mr. Amechi wanda ke wannan tsokaci yayin taron jin ra'ayin jama'a a jiya Litinin a jihar Lagos, ya ce, ma'aikatarsa za ta tabbatar da hada gabar tekun kasar da layin dogo, domin rage dakon kayayyaki ta titunan mota, da ma irin cinkoso da birnin Ikko ke fuskanta sakamakon dakon kayayyaki.
Ya ce, game da hakan, tuni gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan wata kwangila da kamfanin GE, domin farfado da tsohon layin dogo tsakanin Lagos da jihar Kano. Kaza lika kamfanin ya amince ya gina wata jami'a ta harkokin sufuri saboda wannan kwangilar da ya samu.
Har ila yau kamfanin ya amince ya gina wani kamfani na kirar jiragen kasa, da tararon jiragen, da ma sauran sassan jiragen kasa da za a bukata a kasar. (Saminu Alhassan)