in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka rasa matsugunansu a arewa maso gabashin Najeriya ya haura miliyan guda
2016-04-25 09:19:47 cri

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar Najeriya NEMA, ta ce yawan mutanen da suka kaurace wa gidajensu sakamakon tashe-tashen hankalin mayakan Boko Haram, ya kai miliyan daya da dubu 934 da 765. Wadannan mutane dai yanzu haka na zaune a sansanonin 'yan gudun hijira, da wasu sansanonin wucin gadi dake sassan jihohin yankin guda 6.

Sa'ad Bello, shugaban ofishin jiha a hukumar ta NEMA, ya bayyana hakan ga jakadiyar Amurka a MDD Samantha Power, yayin ziyarar aiki da ta kai garin Yola, fadar mulkin jihar Adamawa.

Ya ce, akwai sansanoni na gwamnati 32 a jihohin Borno, da Yobe da Adamawa, wadanda suke kunshe da 'yan gudun hijira 189, 783. Har wa yau akwai wasu sansanonin na wucin gadi 14 a yankunan da aka kwato daga mayakan Boko Haram dake jihar Borno, inda masu neman mafaka 216, 184 ke zaune.

Bello ya kara da cewa, gwamnatin Najeriya na ci gaba da kokarin ganin ta biya bukatun 'yan gudun hijirar na abinci, da ababen masarufi, da magunguna, da tsaro tare da na kula da lafiyar kwakwalwa. Don haka ya bayyana bukatar karin tallafi domin cimma nasara a wadannan sassa, kafin a kai ga mai da 'yan gudun hijirar zuwa yankunansu na asali. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China