Ministan wanda ya bayyana hakan jiya a birnin Ikkon jihar Lagos, ya yi fatan ci gaba da zurfafa huldar cinikayya tsakanin sassan biyu. A cewar sa cimma nasarar fadada alakar Najeriya da Sin ta fuskar cinikayya, zai taimakawa sassan biyu wajen cin gajiya tare, da ma nahiyoyin da suke ciki.
Mr. Enelamah ya kara da cewa Najeriya na iya koyin hadin gwiwa da kasar Sin ta fuskokin tsarin gudanarwa, da yadda Sin ta fidda dunbin al'ummunta daga fatara cikin 'yan shekaru kalilan.
Daga nan sai ya bayyana burin gwamnatin kasar mai ci na zamanintar da masana'antu, da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci, da hada hadar cinikayya yadda ya kamata. Kaza lika a cewarsa Najeriya na da burin rage gibin cinikayya, wanda hakan zai taimaka wajen bude kofar zuba jari, wadda tuni kasar Sin ta bayyana goyon bayan ta ga wannan mataki. (Saminu Alhassan)