Kamfanin Huawei na kasar Sin, wanda ke sahun gaba a fannin fasahar sadarwa, zai horas da matasa 1000 a kasar Najeriya. Mataimaki na musamman ga shugaban tarayyar Najeriya a fannin matasa da dalibai Nasir Adhama ne ya bayyana hakan ga manema labarai, cikin wata sanarwar da ofishinsa ya fitar a ranar Lahadi 24 ga wata.
Adhama ya ce, hakan daya ne daga matakan da gwamnatin Najeriya mai cike dauka, domin magance matsalar karancin ayyukan yi dake addabar al'ummar kasar.
Sanarwar ta ce, za a bayyana lokacin fara gudanar da horon, bayan an tantance wadanda za su amfana. Kaza lika cikin wadanda za su amfana daga horon za a zabi wasu domin karin horo a kasar Sin.
Daga nan sai sanarwar ta bayyana aniyar gwamnatin Najeriya ta ci gaba da aiwatar da makamantan wadannan shirye-shirye, domin baiwa matasa damammaki na magance zaman kashe wando. (Saminu Alhassan)