Ministan wanda ya bayyana hakan yayin taron bayyana wa 'yan kasa halin da gwamnatin ke ciki a watanni 11 da kama aiki, ya ce, irin wadannan balaguro na shugaba Buhari, tuni suka fara haifarwa Najeriya sakamako mai gamsarwa.
Mr. Onyeama ya ce, sanin kowa ne shugaban Najeriya ya fara ne da ziyartar kasashen Chadi, da Kamaru, da sauran makwabtan kasashe, domin aiwatar da tsare-tsaren da za su inganta tsaron kasa, kafin daga bisani ya karkata ga tafiye-tafiyen bunkasa tattalin arziki, duba da yadda farashin mai ke ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya.
Ya ce, ziyarar shugaba Buhari ta baya-bayan nan a kasar Sin, ta samar wa Najeriya damammaki na inganta fannin cinikayya da zuba jari.
Daga nan sai ya jaddada kudurin gwamnatin mai ci na sanya Najeriya zama a sahun gaba a fannin ci gaba a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.(Saminu Alhassan)