in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta dauki matakan dakile yin kutse ta yanar gizo
2016-04-22 10:19:22 cri
A Najeriya hukumar dake kula da cigaban fasahar sadarwa ta kasar NITDA ta fada cewa, a shirye take wajen tunkarar duk wasu hare hare ta hanyar yanar gizo daga dukkan sassa na duniya.

Najeriya ce kasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika, ta fara amfani da tauraron dan adam wajen bibiyar duk wasu hare hare ta shafukan internet, domin dakile duk wani nau'in yin kutse ta yanar gizo, hukumar dai ta ce nauyi ne day a rataya a wuyanta ta kare duk wani nau'i na yin kutse ko hare hare daga dukkan nahiyoyi na duniya.

A sanarwar da hukumar ta fitar, ta bayyana cewar, hukumar ta ware wani yanki na tauraron dan adam wanda zai dinga bibiyar duk wani hari daga duk wani yanki na duniya, musamman bisa la'akari da irin damuwar da kasar ta nuna kan tabbatar da tsaro.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China