in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yi na'am da shirin tsagaita bude wuta a Yemen
2016-03-24 15:11:59 cri
Kwamitin sulhun MDD ya bayar da sanarwa a ranar Larabar data gabata inda ya yi maraba da yadda bangarori daban daban na kasar Yemen suka yi alkawarin tsagaita bude wuta da sake yin shawarwarin shimfida zaman lafiya, kana ya bukaci bangarorin da su dakatar da tada zaune tsaye don share fagen tsagaita bude wutar.

A wannan rana, sojojin hadin gwiwa na kasa da kasa wanda kasar Saudiyya take jagoranta sun bayyana cewa, ana bukatar bangarori daban daban na kasar Yemen, ciki har da halaltacciyar gwamnati a kasar Yemen, da dakarun Houthi su cimma sulhu don warware rikicin siyasar kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China