in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki moon ya nemi da a gaggauta bincike game da harin Yemen
2016-02-29 11:33:00 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi kira da a gaggauta gudanar da bincike game da harin da aka kaddamar a wata kasuwa dake kasar Yemen, wanda ya haddasa kisan fararen hula 32, kana wasu a kalla 41 suka ji raunuka.

Cikin wata sanarwar da kakakin sa ya fitar, Mr. Ban ya yi matukar Allah wadai da harin na kasuwar Khaleq dake arewa maso gabashin birnin Sanaa, wanda ya zama mafi muni tun cikin watan Satumbar bara.

Rahotanni na cewa gamayyar dakarun da kasar Saudiyya ke jagorata ne suka kaddamar da harin ta sama.

Mr. Ban ya nuna damuwar sa game da ci gaba da aukuwar hare hare ta sama da kasa a kasar ta Yemen, duk kuwa da kiraye-kirayen da ake ta yi na tsagaita bude wuta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China