Cikin sanarwar, Ban Ki-moom ya jaddada cewa, ya kamata bangarorin da abun ya shafa su mutunta, da kuma bin dokokin jin kai na kasa da kasa, da kuma dokokin kare hakkin dan Adam, kana su kaucewa kaiwa fararen hula hari, duba da cewa duk harin da aka kai kan fararen hula, laifi ne na keta dokokin jin kai na kasa da kasa. Ya ce kamata ya yi a gudanar da binciki kan wannan lamari yadda ya kamata, ba kuma tare da bata wani lokaci ba.
Kaza lika ya yi kira ga bangarorin da rikicin ya shafa, da su dakatar da daukar matakan soja, yayin da ake kokarin warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar siyasa. (Maryam)